Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Daga Ranar Talatar Da Ta Gabata Ne Dai Aka Fara Aiki Da Hana Daliban Shiga Cikin Jami’ar matukar ba su nuna Shedar cewa an yi musu allurar rigakafi ba.
Sabon tsarin ya kunshi cewa; Wadanda ba su yi rigakafin ba, za su koma gida su yi karatu ne ta hanyar Internet.
Darakta mai kula da harkokin shari’a na jamiar Western Cape Shervaan Rajile ya bayyana cewa; Sabon tsarin yana nufin cewa dalibi zai iya yin rijista da duk wasu shirye-shirye na yin karatu amma fa ba zai shiga cikin harabar jami’a ba sai idan ya yi allurer rigakafi.
Kungiyoyin dalibai na kasar suna cigaba da yin suka akan wannan tsarin da cewa bai yi ba, kuma wasu tsirarun mutane ne da suke jin sun fi suran fahimta su ka fito da shi.”
342/